'Za mu mayar da Gombe cibiyar masana'antun Arewa'

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
'Za mu mayar da Gombe cibiyar masana'antun Arewa'

Jihar Gombe na ci gaba da zawarcin masu zuba jari don buɗe kamfanoni a Cibiyar Masana'antu ta Muhammadu Buhari, wadda hukumomin jihar suka ce za ta ba su damar zuwa kusa da ɗumbin amfanin gonar da Allah Ya hore wa Gombe.