Everton ba ta son rabuwa da Pickford, Man Utd na son Osimhen

Jordan Pickford

Asalin hoton, Getty Images

Everton na shirin gabatar da sabon kwantiragi kan mai tsaron ragarta, Jordan Pickford, ɗan shekara 30 a kokarin ci gaba da rike shi a ƙungiyar. (TBR Football)

Paris St-Germain na son bai wa Arsenal dama na saye ɗan wasanta na Faransa da ba ta wani yayi Randal Kolo Muani, mai shekara 26. (Standard)

Chelsea da Arsenal da Tottenham sun aike wakilansu Club Brugge domin sa ido kan ɗan wasan Belgium Maxim de Cuyper, mai shekara 24. (Caughtoffside)

FC Zurich ta tuntubi Arsenal kan ɗan wasanta na Ingila mai shekara 21, Nathan Butler-Oyedeji. (Football Insider)

An bai wa Manchester United damar saye ɗan wasan gaba daga Najeriya Victor Osimhen a watan Janairu. Napoli na son ta cimma yarjejeniyar musaya da ɗan wasan mai shekara 25 da yanzu ke zaman aro a Galatasaray. (TBR Football)

Kocin Brighton Inigo Calderon, mai shekara 42, ya yi nisa a tattaunawar tafiya Bristol Rovers. (Sky Sports)

Bayern Munich na da kwarin gwiwar saye kan ɗan wasan Jamus mai shekara 21, Florian Wirtz da Bayer Leverkusen ke kokarin tattaunawa da shi kan sabon kwantiragi. (Sky Germany)

Kocin Leicester City Ruud van Nistelrooy na son amfani da alakarsa wajen samun aikin Manchester United a watan Janairu. (Football Insider)

Manchester United ta soma bincike kan wanda zai maye gurbin Erik ten Hag, da zarran tsohon kocinsu ya sa hannu kan sabon kwantiragi a watan Janairu. (Telegraph - subscription required)