Abu uku da wasu jihohin Najeriya suka ƙi amincewa da su a sabuwar dokar haraji
Sabuwar dokar harajin da gwamnatin Najeriya na ci gaba da janyo ta da jijiyoyin wuya daga sassa daban-daban na ƙasar.
Sai dai an fi jin amon yankin arewacin ƙasar wanda kungiyar gwamnoninsa ta fito ƙarara ta nuna adawa da dokar. Ta kuma yi kira ga 'yan majalisun yankin da su yi watsi da ita idan aka gabatar da ita a gaban majalisar dokokin ƙasar.
Ana ganin hakan ba zai sauya komai ba ganin fadar shugaban Najeriya ta fitar da sanarwar cewa ba za ta janye kudurinta ba kan dokar, sai dai a yi mata gyare-gyare.
Me yasa wannan doka ke fuskantar suka tun gabanin gabatar da ita a majalisun dokokin ƙasar?
Kan haka BBC ta tattauna da wani masani ta kuma ta tace wasu abu uku da sune suke jan hankali a sabuwar dokar.
Cire adadin mutane masu yawa da aka yi daga tsarin haraji
"Dokar ta ce duk mutumin da baya karɓar naira miliyan 2,200,000 a matsayin albashinsa a shekara to ba zai biya haraji ba" in ji masanin.
Wannan ɓangare na dokar ya zama babban ƙalubale ga jihohi, ganin cewa mafi ƙarancin albashi bai fi naira budu saba'in ba, 70,000 wadda idan ka buga ta sau 12 za ta baka 840,000.
Gagarumin koma baya hakan zai haifar ga kuɗaɗen da gwamnatocin jiha ke samu daga ma'ikatan jihohinsu.
"Da wuya a ƙarshen shekara ka samu sama da mutum 50,000 a jiha da za su iya samun 2,000,000 idan aka haɗa albashinsu".
Wanda kuma kudin da yake samu ya kai miliyan 2,200,000 zuwa sama zai biyu harajin kashin 15 cikin 100.
Hakan dai ya sa jihohi da dama da suka fahimci wannan ɓangare suka sa ƙafa suka shure dokar.
Me yankinku yake samarwa da ake ɗaukan VAT ciki?
Wannan sashe ma na daga cikin waɗanda suka janyo ce-ce-ku-ce kuma da wuya jihohi da wakilansu su amince da shi a ƙarshe.
A tsarin Najeriya ana raba kason tarayya na kuɗaɗe da ake samu daga jihohi ƙasar, inda ake baiwa Tarayya kashi 52.68, jihohi ana raba musu kashi 26.72 yayin da ƙananan hukumomi ake raba musu kashi 20.60 na kuɗaɗen da aka tattara.
Ana raba waɗannan kuɗaɗe ne la'akari da yawan al'ummar ko wacce jiha.
A yanzu ana son a sauya tsarin zuwa cewa yawan abin da jiha ke iya samarwa a wata yawan abin da za ta riƙa karba.
"Mafi yawan abubuwan da jihohin arewacin Najeriya suke samar da kayan abinci a faɗin ƙasar, kuma abubuwan da suke samar wa babu harajin VAT a kansu, don haka idan aka duba sai ya zama babu abin da suke samarwa ga asusun tarayyar ƙasar.
"Shi yasa ake kiran jihohin arewa ci-ma-zaune, kuma a zahiri ba haka ba ne. Duk yawan geron da ake fitarwa daga Kano ko doya daga Benue babu abin da za a samu na VAT a ciki."
Amma abin tambaya a nan shi ne za a dawo a sanya VAT ne kan wadannan abubuwan da arewacin ƙasar ke fita da shi ke yaya?
Inda za a riƙa karɓar harajin (Derivation)
An yi bayani kan dukkan wasu kalmomi da ke cikin dokar amma ba a yi bayani ba kan kalmar (derivation) sai dai kusan masu fashin baki sun fi mata kallon abin da ka samu na VAT a wata yawan abin da za ka samu na kason gwamnatin tarayya a ƙarshen watan.
Wannan ya kawo magana kan cewa samar da kayayyaki da kuma wuraren da ake amfani da su.
"Dokar ta ce idan kamfani na da hedikwata a wata jiha kuma ya buɗe rassa a wasu wuraren duk yawan VAT da zai samu a waɗannan jihohin da rassan suke, alfanun zai ta fi ne zuwa inda babbar hedikwatarsa take," kamar yadda kwararren ya bayyana.
"Za a riƙa mai dawa jihohin da suke fi samar da VAT kashi 60 cikin 100 na harajin da aka tara wa tarayya gabanin a fara rabawa.
"Akwai rabo da aka yi a watan Satumba, jihar Legas kaɗai ta samu biliyan 45, yayin da jihohi irinsu Kano da Kaduna suka samu biyan 10.
"Ka ga Legas ta samu kusan ninki 5 na wadannan jihohi, wanda kuma a tsari hakan bai dace ba," in ji masanin.
To amma abin da ba a sani ba, duk yawan abubuwan da ake samarwa idan babu masu buƙatarsu to ba su da wani amfani.
Ya kamata a ce an lura da masu amfani da kayan da jihohin domin su ma su riƙa samun nasu rabon.
A nata ɓangaren gwamnatin Najeriya ta hannun shugaban kwamitin sabuwar dokar harajin Taiwo Oyedele ya zanna wasu abubuwa da suke buƙatar 'yan Najeriya su sani a shafinsa na X, ya kuma zayyana su ne ta hanyar tambaya da amsa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da Twitter suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Twitter da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a Twitter
Wasu daga cikin abubuwan da gwamnati ke son a fahimta
Babban maƙasudin sabuwar dokar harajin shi ne sake fasalin yadda ake karɓar harajin domin kawo ƙarshen ƙalubalen masu yawa kamar harajin birane daban-daban, rage nauyin harajin daga kan ɗaiɗaikun 'yan ƙasa da kasuwanci tare da taimakwa wajen kasuwanci domin samar da tattalin arziki da haɓɓakar goben Najeriya.
Rikicin kan harajin VAT tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya ya haifar da wasu manyan hukunce-hukuncen kotu da wasu da har yanzu ake shari'arsu.
Rashin ambatar harajin VAT a kundin tsarin mulkin 1999 ya ƙara rikita lamarin wanda hakan ya haifar da gibi. Bincikenmu ya gano tattara harajin a tarayya ya fi sauki da alfanu.
Da zarar an shawo kan taƙaddamar da ake yi, za a sanya batun VAT a tsarin mulki.
Yadda ake raba shi a yanzu tarayya 15 jihohi kashi 50 sai kuma ƙananan hukumomi kashi 35 zai dakata zai koma tarayya 10 jihohi 55 sai kuma ƙananan hukumomi kashi 35 cikin 100.
Kudurin na neman haɗe wasu hajae-harajen da kuma cibiyoyin karɓar harajin.
Cibiyoyin gwamnati za su mayar da hankali ne kan ayyukan da aka ƙirƙire su su yi maimakon tattara haraji.
Hukumomin da a yanzu suke karɓar haraji da jangali maimakon kuɗaɗen gudanarwa za a riƙa ba su ƙudi ne daga kasafin kowacce shekara.
Ma'aikatan da albashinsu shi ne mafi ƙaranci waɗanda suka kai kashi ɗaya cikin uku za su zama ba za su biya harajin komi ba, yayin da masu ɗaukar madaidaici da tsakatsaki dole su biya.
Cikin sauyin akwai karɓar harajin sufili daga abinci, ɓangaren ilimi da lafiya da kuma sufuri.