Gane Mini Hanya tare da gwamnan jihar Zamfara 21/12/2024
Gane Mini Hanya tare da gwamnan jihar Zamfara 21/12/2024
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya ce har yanzu yana kan matsayarsa, cewa ba zai yi sulhu da ƴan fashin daji ba.
Yayin zantawarsa da BBC gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matsaya ne ganin cewa a bayan an sha yin sulhu da 'yan bindigar, amma ba sa mutunta alƙawurran da aka yi da su a baya.
''An yi sulhun nan a baya ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, amma an kasa cimma ake abin da ake so'', in ji gwamnan.