Rasha ta musanta cewa matar Assad ta nemi ya sake ta

Asma ta auri Assada a 2000

Asalin hoton, Getty Images

Matar hamɓararryen Shugaban Ƙasar Syria, Bashar al-Assad ba ta nemi saki ba, kamar yadda kakakin Kremlin ya bayyana.

Wasu rahotanni daga kafofin watsa labarai daga Turkiyya ne suka ruwaito cewa Asma al-Assad, wadda asali ƴar Burtaniya ce, ta buƙaci mijinta ya sake ta domin ta bar Rasha, ta koma ƙasarta ta asali.

Da aka tambaye shi a wani taron manema labarai, Dmitry Peskov ya ce, "labaran ba na gaskiya ba ne."

Ya kuma ƙaryata rahotannin cewa an ɓoye Assad a Moscow, sannan an ƙwace kadarorinsa.

Rasha ta kasance ƙawar Syria a zamanin mulkin Assad, inda ta riƙa ba shi gudunmuwar soji a lokacin yaƙin basasa.

Duk da cewa ƴar asalin ƙasar Burtaniya ce, amma sakataren harkokin wajen Burtaniya ya taɓa faɗa a baya cewa ba za su bari ta dawo ƙasar ba.

Da yake jawabi a watan jiya a gaban majalisa, David Lammy, ya ce, "zan iya tabbatar muku cewa akwai takunkumi a kanta, kuma ba ma maraba da ita a Burtaniya."

Ya ƙara da cewa zai yi duk abin da zai iya yi domin tabbatar da cewa babu wani ɗan gidan Assad da ya koma Burtaniya da zama.

Ita dai mai ɗakin Assad ɗin ta kasance mai ƙasa guda biyu - Syria da Burtaniya, to amma sakataren harkokin wajen Burtaniya a baya ya ce ba za a ƙyale ta ta koma Burtaniyar ba.

Da yake magana a majalisar dokoki a farkon watan nan, David Lammy ya ce "I na son tabbatar da cewa an sanya mata takunkumi sannan kuma ba ma maraba da ita a nan Burtaniya."

Ya ƙara da cewa da zai iya duk "abin da zai iya a iya ikonsa" domin tabbatar da cewa babu wani daga iyalan Assad da "zai shigo Burtaniya."

A wata sanarwa da aka alaƙanta da Bashar al-Assad makon da ya gabata, ya ce bai taɓa ƙudirin guduwa daga Syria ba, amma kuma aka ɗauke shi a jirgi daga sansanin sojojin Rasha bisa buƙatar Rashar.

Wace ce Asma al-Assad?

Asma ƴar Syria ce haihuwar Burtaniya

Asalin hoton, Getty Images

An dai haifi Asma al-Assad ƴar asalin Syria mai shekara 49 a Burtaniya, inda mahaifanta suka rayu a yammacin London.

Ta koma Syria a shekarar 2000 a lokacin tana da shekara 25 inda kuma ta auri Assada ƴan watanni kaɗan bayan ya gaji mahaifinsa a matsayin shugaba.

A tsawon shekarunta 24 na kasancewarta mai ɗakin shugaban ƙasa, Asma ta zama abar tattaunawa a kafafeb watsa labarai na ƙasashen yamma.

A 2016, Asma Assad ta shaida wa kafar talbijin ta Rasha cewa ta yi watsi da wata buƙatar tserartar da ita da aka yi daga yakin da ke faruwa a Syria domin ci gaba da kasasncewa da mai gidanta.

Ta sanar da cewa ta samun kulawa dangane da cutar dajin mama da take fama da ita a 2018 sannan ta ce ta samu lafiya shekara guda bayan nan.

An kuma same ta da cutar kansar jini sannan ta fara yin maganin cutar a watan Mayun wannan shekara kamar yadda ofishin tsohon shugaban ya sanar.

Wata sanarwa ta ce Asma za ta "janye jikinta daga abubuwan jama'a" na ɗan wani lokaci.