Yadda 'Yan Najeriya ke Buya a Amurka bayan Trump Ya Zafafa Dokoki

Yadda 'Yan Najeriya ke Buya a Amurka bayan Trump Ya Zafafa Dokoki

  • 'Wasu yan Najeriya sun daina fita bainar jama'a saboda tsoron kama su da korarsu daga Amurka bayan Donald Trump ya tsaurara matakai
  • Rahotanni na nuni da cewa kusan 'yan Najeriya 3,690 ne ke fuskantar barazanar kora daga kasar Amurka bisa zargin zama ba bisa ka'ida ba
  • Wasu 'yan Najeriya sun bayyana cewa halin da suke ciki ya fi musu dawowa Najeriya da ke fama da matsaloli tsaro da tattalin arziki da sauransu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - 'Yan Najeriya da ke zaune a Amurka ba bisa ka’ida ba sun bayyana cewa sun takaita zirga-zirgarsu a wuraren jama'a domin guje wa kamun jami'an hukumar kula da bakin haure.

Wannan mataki ya biyo bayan sababbin manufofin gwamnatin shugaba Donald Trump na tsaurara dokokin shige da fice, lamarin da ke sanya fargaba ga bakin hauren da ba su da takardu.

Kara karanta wannan

Abin na manya ne: Yan Majalisa sun barke da zanga zanga a Abuja, sun jero bukatu

Tinubu Trump
'Yan Najeriya sun fara fakewa a gida a Amurka. Hoto: Donald J. Trump|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta yi hira da wasu daga cikin 'yan Najeriya a Amurka kuma sun bayyana halin da suke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin bakin hauren sun daina zuwa wuraren aiki da ibada tun bayan da Trump ya karbi mulki, domin kada a kama su.

Duk da haka, suna fatan shari'o'in da aka shigar a kotu kan manufofin shige da ficen gwamnatin Trump za su iya rage wa bakin hauren wannan matsin lamba.

'Yan Najeriya 3,600 na fuskantar barazana

Wani rahoto daga Hukumar Kula da Shige da Fice ta Amurka (ICE) ya nuna cewa akalla 'yan Najeriya 3,690 na fuskantar barazanar korar dole daga kasar.

Takardar da hukumar ta fitar ta bayyana cewa kasashen Mexico da El Salvador ne ke kan gaba wajen yawan wadanda ake shirin kora daga Amurka.

A cewar rahoton, jimillar baki 1,445,549 da ba 'yan kasa ba ne ke kan jerin wadanda aka yanke musu hukuncin kora daga Amurka tun daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan

Tankar fetur ta yi bindiga a gidan mai a Jigawa, ta tayar da gobara

Wannan yawan ya hada da 'yan Najeriya da sauran kasashen Afirka, inda suka bayyana damuwarsu kan yiwuwar komawa Najeriya da ke fama da matsalolin tattalin arziki da tsaro.

Halin da 'yan Najeriya ke ciki a Amurka

Wani dan Najeriya da ke zaune a Tampa, Florida, ya ce tun bayan da Trump ya karbi mulki ya daina fita aiki domin guje wa kama shi da jami'an ICE za su iya yi.

Dan Najeriyan ya ce:

“Tun bayan da Trump ya hau mulki kuma ya fara aiwatar da barazanar korar baki, wasu daga cikinmu mun daina zuwa aiki saboda jami'an ICE na iya kai samame a wuraren aiki."

Ya kara da cewa ya daina zuwa coci da sauran wuraren jama'a saboda tsoron a kama shi.

“Ni da wasu 'yan Afirka da muke aiki tare a masana'anta mun daina fita. Ba na zuwa coci saboda ana iya kama mutum a wuraren ibada.

Kara karanta wannan

Matar Tinubu ta ba da mamaki a Kwara, ta fita a mota ta tattauna da dalibai

"A halin yanzu, zaman gida shi ne mafita mafi aminci.”

Sai dai ya yi fatan cewa suna tsammanin za a rage farautar baki nan gaba kadan kamar yadda aka taba yi a baya.

Vanguard ta wallafa cewa ya ce:

“Mun tsira daga matakan korar da gwamnatin Obama ta yi, za mu tsira daga wannan ma.
"Muna fatan shari'o'in da ake yi kan dokokin shige da ficen za su iya rage wannan matsin lambar."

Matsalolin samun takardu a Amurka

Wani dan Najeriya da ke zaune a Columbus, Ohio, ya ce shi ma ya daina zuwa aiki mako guda bayan rantsar da Trump saboda tsoron kora.

A cewarsa, wadanda suka fara fuskantar kora daga Amurka su ne wadanda ke da laifuffuka, amma yanzu an fara aiwatar da korar baki da ba su da wani laifi.

Ya kuma bayyana cewa duk kokarinsa na samun takardun zama a kasar sun ci tura, inda ya ce ya kashe kusan $30,000 ba tare da ya samu nasara ba.

Kara karanta wannan

Majalisar dokokin Kano ta fusata bayan gano abin da ake yi a gidajen da Kwankwaso ya gina

Ya ce:

“Na bar Najeriya zuwa Amurka a shekarar 2013, kuma tun daga lokacin nake kokarin samun takardun zama."
"An zambace ni ta hanyar aure da wasu hanyoyi daban-daban. A kokarin da nake yi, na rasa kusan $30,000."

Trump ya dakatar da tallafin lafiya

A wani rahoton, kun ji cewa Najeriya na fuskantar barazana a harkokin lafiya bayan shugaba Donald Trump ya dakatar da tallafin kanjamau.

Shugaba Donald Trump ya ce ba zai cigaba da kashe makudan kudi domin tallafawa kasashe ba matukar 'yan Amurka ba za su amfana ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. [email protected]