Jump to content

Paulinus Igwe Nwagu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Paulinus Igwe Nwagu
mutum
Bayanai
Bangare na Majalisar Wakilai (Najeriya)
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Suna Paulinus (mul) Fassara
Shekarun haihuwa 12 ga Yuni, 1959
Sana'a ɗan siyasa
Muƙamin da ya riƙe mamba a majalisar dattijai ta Najeriya da mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,
Ɗan bangaren siyasa Peoples Democratic Party

Paulinus Igwe Nwagu (an haife shi a ranar 12 ga watan Yunin a shekara ta 1959) ɗan siyasar Najeriya ne wanda ya kasance wakilin Mazaɓar Ezza North/Ishielu na jihar Ebonyi, Najeriya a majalisar wakilai. A zaɓen ƙasa na watan Afrilun shekarar 2011, an zaɓe shi Sanata mai wakiltar Ebonyi ta tsakiya mai neman tsayawa takara a jam’iyyar PDP.

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Nwagu a ranar 12 ga watan Yuni a shekara ta 1959, a jihar Ebonyi. Ya samu digirin farko a fannin Kimiyyar Siyasa. Ya kasance Kansila na Ƙaramar Hukumar Ezza ta Arewa daga shekara ta 1990 zuwa 1993 kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Ezza ta Arewa daga shekara ta 1999 zuwa 2002.[1]

Sana'ar siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

An zaɓi Nwagu a matsayin ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Ishielu ta Ebonyi ta Ezzra ta Arewa a cikin watan Afrilun shekarar 2007, a tsarin PDP. A majalisar, an naɗa shi a kwamitocin kula da matasa da ci gaban al'umma, siyan kayayyakin jama'a, harkokin ƴan sanda, albarkatun man fetur (Dowstream), muhalli da gaggawa & Gudanar da Bala'i.[2] Ya kasance shugaban kwamitin majalisar wakilai kan raya karkara. A cikin shekarar 2009 hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa EFCC ta kama Igwe tare da tsare shi a gidan yari na Kuje da ke Abuja bisa zarginsa da hannu a badaƙalar wutar lantarki ta Naira biliyan 5.2 (dala miliyan 34.66).[3][4]

A zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP a cikin watan Janairun shekarar 2011, ɗan takarar kujerar Sanatan Ebonyi ta tsakiya, an ayyana Nwagu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar PDP sakamakon ƙauracewa zaɓen da wasu ƴan takara suka yi kan wasu kura-kurai da suka haɗa da yin amfani da katin zaɓe da aka yi nufin jihar Kwara don gudanar da zaɓen Ebonyi ta tsakiya.[5][6] Ya lashe zaɓen a cikin watan Afrilun shekarar 2011 da ƙuri'u 55,016 a jam'iyyar PDP. Ugo Chima na jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP) ya samu ƙuri'u 41,096.

A cikin watan Mayun shekarar 2022, ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takara a zaɓen gwamna a jihar Ebonyi.[7] Ƴan takara 14 ne suka fafata da su a matsayin ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamna na shekarar 2023; tara daga yankin Sanata na Ebonyi ta Arewa da suka haɗa da Nwagu, huɗu daga Ebonyi ta tsakiya da ɗaya daga Ebonyi ta Kudu.[8] Daga baya Obinna Ogba daga Ebonyi ta tsakiya ne ya lashe zaɓen fidda gwani.[9]

  • Jerin mutanen jihar Ebonyi
  1. https://tribuneonlineng.com/nkata-nwagu-emerges-apga-pdp-deputy-gubernatorial-candidates-in-ebonyi/
  2. https://web.archive.org/web/20100718174336/http://www.speakersoffice.gov.ng/constituencies_ebonyi_3.htm
  3. https://web.archive.org/web/20160303224213/http://www.businessdayonline.com/NG/index.php/news/latest/2742-efcc-may-make-more-arrests-to-arraign-ugbane-elumelu-others-today
  4. https://web.archive.org/web/20120329060746/http://www.tribune.com.ng/index.php/news/18917-shoddy-jobs-nass-threatens-to-sanction-erring-contractors
  5. https://web.archive.org/web/20151208095811/http://odili.net/news/source/2011/jan/10/5.html
  6. https://web.archive.org/web/20120314124630/http://www.worldstagegroup.com/worldstage/index.php?active=news&id=1626
  7. https://www.thisdaylive.com/index.php/2022/05/02/2023-ill-reclaim-ebonyi-back-to-pdp-says-senator-igwe-nwagu/
  8. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-07-18. Retrieved 2023-04-09.
  9. https://tribuneonlineng.com/ogba-emerges-pdp-gubernatorial-flagbearer-in-ebonyi/