Kagarko
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Kagarko | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jihar Kaduna | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 1,864 km² | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Kagarko karamar hukuma ce a jihar Kaduna, a Najeriya. Hedkwatarta tana cikin garin Kagarko. Ta mamaye yanki mai girman 2,356 km2 da yawan jama'a 239,058 dangane da ƙidayar 2006. Nasara Rabo ke jagorantar Ƙaramar hukumar. Lambobin tura saƙo zuwa yankin sune 802.
Iyakoki
[gyara sashe | gyara masomin]Karamar hukumar Kagarko (Wogon) tana da iyaka da karamar hukumar Kachia a arewa, karamar hukumar Jaba daga gabas, jihar Neja zuwa yamma da kuma babban birnin tarayya Abuja a kudu.
Yaruka/Kabilu
[gyara sashe | gyara masomin]Mutanen dai manoma ne. Mutanen Batinor (Koro) sune ke da rinjaye a yankin. Sauran sun hada da Fulani, Gbagyi, Ham, Hausa da Adara . Suna aiki tukuru kuma galibi manoma, kusan kashi 70% na ginger da ake nomawa a jihar Kaduna daga Kagarko suke.
Sanannun mutane a Kagarko
[gyara sashe | gyara masomin]- Nenadi Usman. Tsohuwar sanatan a kudancin Kaduna kuma tsohuwar ministar kuɗi
- Caleb Zagi. Tsohon sanatan a kudancin Kaduna. #Muhammad Bello Umar Kagarko. Tsohon kwamishina na kana nan hukomomi kuma kwamishina na ilimi.
Kujerun gargajiya
[gyara sashe | gyara masomin]Kagarko ya ƙunshi sarakuna uku:
- Masarautar Kagarko : Mai martaba Sarkin Kagarko Alh. Sa’ad Abubakar, mai hedikwata a Garin Kagarko;
2. Jere Royaldom : Sarkin Jere, Marigayi Dr. Sa'ad Usman (OFR)
3. Koro masarautar : Ere-Koro, Ere Yohanna Akaito (JP), mai hedikwata a Kurmin Jibril (Maraban Kubacha) ;