British Columbia
British Columbia | |||||
---|---|---|---|---|---|
|
|||||
| |||||
| |||||
Kirari | «Splendor Sine Occasu» | ||||
Official symbol (en) | Steller's Jay (en) , Kermode bear (en) , Oncorhynchus (en) , Cornus nuttallii (en) , jade (en) da Thuja plicata (mul) | ||||
Suna saboda | British Isles (en) da Columbia District (en) | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Kanada | ||||
Babban birni | Victoria (en) | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 5,000,879 (2021) | ||||
• Yawan mutane | 5.29 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 944,735 km² | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Pacific Ocean | ||||
Wuri mafi tsayi | Mount Fairweather (en) (4,671 m) | ||||
Wuri mafi ƙasa | Pacific Ocean (0 m) | ||||
Sun raba iyaka da |
Alberta (mul) (1 Satumba 1905) Montana (8 Nuwamba, 1889) Alaska (3 ga Janairu, 1959) Yukon (en) (13 ga Yuni, 1898) Washington (11 Nuwamba, 1889) Idaho (3 ga Yuli, 1890) Northwest Territories (en) | ||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Colony of British Columbia (en) | ||||
Ƙirƙira | 1871 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Tsarin gwamnati | parliamentary democracy (en) | ||||
Majalisar zartarwa | Government of British Columbia (en) | ||||
Gangar majalisa | Parliament of British Columbia (en) | ||||
• monarch of Canada (en) | Charles, Yariman Wales | ||||
• Premier of British Columbia (en) | David Eby (en) (18 Nuwamba, 2022) | ||||
Ikonomi | |||||
Nominal GDP (en) | 309,327,000,000 $ (2020) | ||||
Kuɗi | Canadian dollar (en) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lambar aika saƙo | V | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | 236, 778, 250 da 604 | ||||
Lamba ta ISO 3166-2 | CA-BC | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | www2.gov.bc.ca… | ||||
British Columbia, wadda aka fi sani a saukake da BC, ita ce yammacin Kanada, tana tsakanin Tekun Pasifik da Dutsen Rocky . Tana da yanayi daban-daban, waɗanda suka haɗa da rairayin bakin teku masu duwatsu, rairayin bakin teku masu yashi, dazuzzuka, tafkuna, tsaunuka, hamadar cikin ƙasa , kuma tana da iyaka da lardin Alberta zuwa gabas, yankuna na Yukon da Yankunan Arewa maso Yamma zuwa arewa, da jihohin Amurka na Washington, Idaho da Montana a kudu da Alaska a arewa maso yamma. Tare da kiyasin yawan mutane kimanin 5.3 miliyan a shekarar qidaya na 2022, ita ce lardin Kanada na uku mafi yawan jama'a . Babban birnin British Columbia shine Victoria kuma birni mafi girma shine Vancouver . Vancouver shine yanki na uku mafi girma a cikin Kanada ; a ranar 2021 ya kasance mutane miliyar biyu da dubu dari shida a Metro Vancouver .
Asali
[gyara sashe | gyara masomin]Sarauniya Victoria ta zaɓi sunan ne, tun lokacin da Turawan mulkin mallaka na British Columbia a shekarar (1858–1866), watau, ya zama mulkin mallaka na Burtaniya a shekarar 1858. [1] Yana nufin Gundumar Columbia, sunan Birtaniyya a yankin da Kogin Columbia yake, a kudu maso gabashin British Columbia, wanda shine sunan da aka riga aka yi wa Sashen Yarjejeniyar Columbia na Kamfanin Hudson's Bay . Sarauniya Victoria ta zaɓi gundumar British Columbia don bambanta abin da ke cikin sashin Burtaniya na Gundumar Columbia daga Amurka ("American Columbia" ko kuma "Kudancin Columbia"), wanda ya zama yankin Oregon a ranar 8 ga watan Agusta, shekara ta 1848, sakamakon yarjejeniyar.
Iyaka
[gyara sashe | gyara masomin]British Columbia tana da iyaka daga yamma da Tekun Pasifik da jihar Alaska ta kasar Amurka, zuwa arewa da Yankunan Arewa maso Yamma, daga gabas da lardin Alberta, daga kudu kuma tana da iyaka da jihohin Amurka na Washington, Idaho . da Montana . An kafa iyakar kudancin British Columbia ta yarjejeniyar Oregon a shekarar 1846, kodayake tarihinta yana da alaƙa da ƙasashe har zuwa kudancin California . Yankin British Columbia yana da kilomita 944,735 . Garin gaɓar tekun British Columbia ya kai fiye da kilomita 27,000, kuma ya haɗa da tudu masu zurfi, tsaunuka da kusan tsibiran 6,000, waɗanda yawancinsu ba kowa bane. Lardi ne kawai a cikin Kanada da ke iyaka da Tekun Pacific .