Anisul Islam Mahmud
Anisul Islam Mahmud | |||||
---|---|---|---|---|---|
ga Janairu, 2014 - District: Chittagong-5 (en)
District: Chittagong-5 (en) | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Chittagong, 20 Disamba 1947 (76 shekaru) | ||||
ƙasa |
Bangladash Pakistan | ||||
Harshen uwa | Bangla | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
University of Dhaka (en) University of Essex (en) | ||||
Harsuna | Bangla | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Employers |
University of Dhaka (en) University of Hertfordshire (en) | ||||
Imani | |||||
Addini | Musulunci | ||||
Jam'iyar siyasa | Jatiya Party (en) |
Anisul Islam Mahmud(an haife shi 20 Disamba 1947) tsohon ministan muhalli ne da gandun daji a majalisar ministocin Bangladesh. Ya taɓa riƙe muƙamin Ministan Harkokin Waje daga Yuli 1985 zuwa Disamba 1990.
Mahmud ya yi karatu a Jami’ar Dhaka (BA Economics, 1969), Jami’ar Quaide Azam a Karachi (MSc Economics) da Jami’ar Essex (MA Economics, 1972). An kira shi zuwa Bar a Lincoln's Inn acikin 1975. Ya kasance Malamin Ilimin Tattalin Arziki a Jami'ar Dhaka daga 1969 zuwa 1970, Babban Jami'in Bincike kan Tattalin Arziki a Jami'ar East Anglia daga 1972 zuwa 1973, kuma malami a fannin tattalin arziki a Jami'ar Hertfordshire daga 1973 zuwa 1977.
Ya zama dan majalisa mai wakiltar Chittagong-5 a 1979, kuma an sake zabe shi a 1986 da 1988. Ya sake tsayawa takara a zaben watan Yuni na 1996, amma ya sha kaye a hannun Syed Wahidul Alam. Ya zama MP na Chittagong-4 acikin 2008, an zaɓe shi ba tareda hamayya da Chittagong-5 ba a 2014, kuma an sake zaɓen sa a 2018.