Abuja
Abuja | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Jihohin Najeriya | Babban Birnin Tarayyan Najeriya, | ||||
Babban birnin | |||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 1,693,400 (2022) | ||||
• Yawan mutane | 2,375.04 mazaunan/km² | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 713,000,000 m² | ||||
Altitude (en) | 360 m | ||||
Bayanan tarihi | |||||
Ƙirƙira | 1828 | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | fcta.gov.ng |
[[File:Abuja, Federal Capital Territory 3.jpg|thumb|Cikin Birnin Abuja] Abuja[1] Itace babban birnin tarayya, kuma na takwas a girma a Najeriya[2]. Birnin na nan a tsakiyar ƙasar Najeriya, a cikin Birnin Tarayya (FCT), kuma tsararran birni ne da aka zana a tsakanin shekarun 1980s, wanda mai zane Architect Kenzo Tange ya zana ta.[3] Ta zama babbar birnin Najeriya bayan tsohuwar babban birnin Legas[4] a ranar 12, ga watan Disamba shekara ta Alif 1991 .[5]
Birnin ya koma na tarayya ne tun a lokacin mulkin Gen. Ibrahim Babangida[6] a shekarar alif ɗari tara da casa'in da ɗaya (1991)[7] wanda kafin lokacin birnin tarayyar ya kasance a birnin Legas[8] dake kudu maso yammacin Najeriya. Birnin Abuja ya kasance birni ne gagara-misali saboda birnin ya ƙunshi abubuwa da dama wanda ido ne kaɗai zai iya tabbatar da haka. Manƴan Ma'aikatu, Makarantu[9], filayen jiragen sama, da kuma filin wasa Babba, da dai sauran manya-manyan ma'aikatun gwamnati wanda suke juya akalar ƙasar baki ɗaya. A cikin birnin Abuja akwai mutane a kalla 776,298, a kiɗayar shekarar 2006, kasan cewar birnin na tarayya[10] ne wato ya tara duk jinsin mutane[11] da ƙabilun[12] dake Najeriya gaba ɗaya, ko wacce jiha a Najeriya tana da wakilai a sassa daban-daban a cikin Abuja domin ganin sun wakilci jihar su a fage da dama don cigaban jihar su. A cikin birnin Abuja akwai wuraren shaƙatawa da dama da wuraren buɗe ido musamman ga baƙi, waɗanda suke muradin kashe kwarkwatar ido ta fagen kallon abubuwan ban al'ajabi, da ɗebe kewa.
Babban al'amari game da labarin ƙasa na Abuja (wato geography) sun haɗa da Aso Rock[13], gidan shugaban ƙasa (presidential complex), Majalisar dokoki (National assembly),[14] Kotun ƙoli (supreme court), Sannan yawancin birnin ya mike har zuwa kudancin dutsen, Sannan kuma Zuma Rock[15] wanda ke arewacin birnin a bisa babban titin Kaduna.[16]
Manyan wuraren bautan sun haɗa da babban masallaci[17] da babban chochi na birnin Abuja, wato Nigerian National Central Mosque da Nigerian National Christian Centre. Birnin na hada-hada daga filin jirgin saman Abuja wato Nnamdi Azikiwe International Airport. Abuja tana ɗaya daga cikin manyan birane da aka tsara kuma ɗaya daga cikin mafi arziƙi.[18]
Abuja itace cibiyar gudanarwa da siyasa na Najeriya. Har wayau tana ɗaya daga cikin manyan birane na Afurka musamman matsayin Najeriya a harkokin siyasa da ci gaba.[19] Abuja tana da mahimmanci a harkokin ganawa watau meeting kamar 2003, Commonwealth Heads of Government meeting da kuma 2014, World Economic Forum (Africa) meetings.[20][21]
Tarihi.
[gyara sashe | gyara masomin]Garin Abuja a farkon ƙarni na 20, sunan wani gari ne yanzu da ake kira Suleja.[22] Asalin mazauna Abuja Gwari ne, wato mutanen Gbagyi, wanda Gbagyi ne yaren farko na garin sai kuma sauran yarika kaman Bassa, Gwandara, Gade, Dibo, Nupe da kuma Koro.[23] An samar da babban birnin a dalilin rabe-raben harsuna a Najeriya.[24] Sauran dalilan kuma sun haɗa da yawan mutanen Legas, wanda ke jawo cunkuso a garin. Sannan bugu da ƙari garin Legas na samun haɓakar kasuwanci cikin sauri, wannan dalilai suka jawo aka maido da babban birnin zuwa Abuja.[25] Wannan tsari da aka bi iri ɗaya ne da yadda Brazil suka tsara babban birninsu Brasilia.
Gwamnatin Soji ta Najeriya a ranar 4, ga watan Febrerun shekara ta 1976, ta fidda tsarin doka mai lamba 6, acikin kundin tsarin mulki wacce ta cire Legas a matsayin babban birnin kasan zuwa Abuja.[26][27] Gwamnatin Soji na Murtala Muhammed da kuma Olusegun Obasanjo ne suka fidda asalin aikin tsarin samar da babban birnin Abuja wanda gamnatin farar hula ta Shehu Shagari ta karasa.[28]Tsarin gine-gine ya fara acikin shekarun 1970s, amma a dalilin matsalar kudade na siyasa, an karasa aikin a shekarun 1980s. Maido babban birnin Najeriya zuwa Abuja ya jawo rikici sosai kuma babban dan-adawan wannan canji shine Obafemi Awolowo.[29] Obafemi Awolowo ya kasance dan siyasan Najeriya mai kuma wakiltan yarbawa acikin kin yarda da maido babban cibiyar kasan daga Legas zuwa Abuja. A lokacin da ake yakin neman zabensa na shugaban kasa, ya sha alwashin cewa idan ya zamo shugaba zai gayyato kamfanin "Walt Disney Corporation" don su mayar da Abuja wajen shakatawa.[30] Amma kash, samun nasarar shugaban ƙasan farar hula na farko wato shehu shagari ya sa an fara ci gaba da habaka gine-gine a babban birnin inda ya nemi 'yan kwangila da 'yan kwadago da su dage wajen kammala aikin a cikin sauri. Bayan dawowarsa ya nuna rashin gamsuwar sa akan yadda aikin ya dau tsawon lokaci ga Alhaji Abubakar Koko.[31]
An baiwa kamfanin International Planning Associates (IPA) kwangilar kawo tsarin zanen Abuja a shekarar 1977, wanda sashin gwamnatin tarayya watau Federal Capital Development Authority (FCDA) suka bada kwangilan.[32]A yanda nasaban tsarin yarjejeniyar ta nuna, tsarin ya klƙunshi al'amurra daban daban, wanda suka hada da zaban wajen da zai zama gidan gwamnati, tsarin yadda yankuna da birane zasu kasance da kuma kundi na tsare-tsare da na cigaba.[33]
Gudanarwa.
[gyara sashe | gyara masomin]Abuja Municipal Area Council ke gudanar da harkokin birnin Abuja. Bugu da ƙari akan harkokin ayyukan gwamnati birnin shine cibiyar gwamnatin tarayyar Najeriya kuma har wayau tushen siyasa da gudanarwa na gwamnatin ƙasar.
Hukumar babban birnin tarayya (FCTA) ce ke tafiyar da babban birnin tarayya, wanda ministan da shugaban kasa ya zaba na FCT ke shugabanta. Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCDA) ce ke kula da ayyukan gine-gine da abubuwan more rayuwa na yankin. A yanzu haka tsohon gwamnan Rivers Nyesome Wike shine ministan babban birnin tarayya.[34]
Ƙananan hukumomi.
[gyara sashe | gyara masomin]Babban Birnin tarayya Abuja nada ƙana nan hukumomi guda Shida (6)
1.Abaji.
2.Garki (Abuja Municipal).
3.Bwari.
4.Gwagwalada.
5.Kuje.
Haɗin fili na waɗannan kananan hukumomi 6 kusan kilomita 7,290 ne.
Sassan Abuja.
[gyara sashe | gyara masomin]Abuja tana da sassa wato (districts) da dama tun daga Phase 1 har zuwa phase 3 sune kamar haka:[36]
SASSA NA PHASE 1
[gyara sashe | gyara masomin]- Central cadastral zone A00
- Garki I District cadastral zone A01
- Wuse 1 District cadastral zone A02
- Garki II District cadastral zone A03
- Asokoro cadastral zone A04
- Maitama Districts cadastral zone A05
- Maitama cadastral zone A06
- Wuse II District cadastral zone A07
* Wuse II cadastral zone A08
- Guzape District zone A09
SASSA NA PHASE 2
[gyara sashe | gyara masomin]- kukwuaba cadastral zone B00
- Gudu cadastral zone B01
- Durumi cadastral zone B02
- Wuye cadastral zone B03
- Jabi cadastral zone B04
- Utako cadastral zone B05
- Mabushi cadastral zone B06
- Jahi cadastral zone B08
- Kado cadastral zone B09
- Dakibiyu cadastral zone B10
- Kaura cadastral zone B11
- Duboyi cadastral zone B12
- Gaduwa cadastral zone B13
- Dutse cadastral zone B14
- Katampe Ext cadastral zone B19
SASSA NA PHASE 3
[gyara sashe | gyara masomin]- Institution and Research Cadastral Zone C00,
- Karmo Cadastral Zone C01,
- Gwarimpa Cadastral Zone C02.
- Dape Cadastral Zone C04,
- Kafe Cadastral Zone C05
- Nbora Cadastral Zone C06,
- Galadimawa Cadastral Zone C07,
- Dakwo Cadastral Zone C08,
- Lokogoma Cadastral Zone C09,
- Wumba Cadastral Zone C10,
- Idu Industrial Cadastral Zone C16
Manyan wurare a Abuja
[gyara sashe | gyara masomin]- Gidan Shugaban kasa (Villa)
- Majalisar Dattawa
- Majalisar Wakilai (NASS)
- Babban kotun koli (supreme court)
- Babban Bankin Nijeriya (CBN)
- Babban ofishin sojoji
- Babban ofishin yan sanda na kasa
- Ma'aikatar sufuri ta kasa
- Babban ofishin kwastam na kasa
- Ofishin gamayyar Afrika (ECOWAS)
- Massallacin Tarayya
- Massallacin An Noor
Wajen Gari
[gyara sashe | gyara masomin]Garuruwan da suke waje da birnin Abuja[37]
- Dawaki
- Gwagwalada
- Karu
- Kubwa
- Mpape
- Nyanya.
Labarin Ƙasa.
[gyara sashe | gyara masomin]Garin Abuja na da bisan kimanin mita 360m.
Chanjin yanayi a sashen Abuja.
[gyara sashe | gyara masomin]
Abuja a tsarin rabe-raben Koppen ta faɗa a ajin tropical wet and dry climate (Köppen: Aw). Garin na fuskantar yanayi iri uku, sanyi, zafi da kuma lokacin ɗumi da ruwan sama. A tsakanin waɗan nan yanayi akwai lokacin sanyi da hazo.
Ruwan sama a Abuja yana farawa ne daga watan Aprilu sannan ya ƙare a watan October, a yayin da zafin hasken rana yake kaiwa makin 28 °C (82.4 °F) zuwa 30 °C (86.0 °F) sannan kuma sanyin dare a maki mafi ƙarancin yana kaiwa 22 °C (71.6 °F) zuwa 23 °C (73.4 °F). Amma a lokacin rani, zafin hasken rana a bisa maki mafi girma yana kaiwa 40 °C (104.0 °F) amma yanayin yana sauƙi da dare akan makin ma'aunin celcius 12 °C (53.6 °F). har zuwa ƙarshen dare yana kaiwa 30 °C (86.0 °F). wannan shine adadin makin sauyin yanayi da sashin birnin Abuja ke fuskanta a taƙaice.
Sadarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Tashoshin Gidan Radio a yankin Abuja
[gyara sashe | gyara masomin]- 88.9 - Brila FM (Abuja) - sports
- 92.1 - Vision FM
- 92.9 - Kapital FM
- 93.5 - ASO Radio
- 94.7 - Rhythm FM (Abuja)
- 96.9 - Cool FM (Abuja)
- 98.3 - Hot FM (Abuja)
- 99.5 - Wazobia FM (Abuja)
- 99.9 - Kiss FM (Abuja)
- 100.5 - RayPower FM (Abuja)
- 104 - Love FM (Abuja)
- 95.1 - Nigeria Info
- 106 - WE FM
Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin][[File:Secret garden in Riverplate park - Abuja.jpg|Secret garden in Riverplate park - Abuja
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://dailytrust.com/minimum-wage-governors-emergency-meeting-kicks-off-in-abuja/&ved=2ahUKEwjYzaXC-PqGAxXZRkEAHfCqD3cQxfQBKAB6BAgsEAE&usg=AOvVaw3eI6Yzjz4joThFGhvxVhCk
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://punchng.com/nigeria-to-install-terrestrial-fibre-optic-infrastructure-edun/%3Famp&ved=2ahUKEwjfu8v1-PqGAxUWT0EAHXxpAfwQyM8BKAB6BAgKEAI&usg=AOvVaw3-Av8oGTAPLbKNZqpUfkXX
- ↑ "Life of poverty in Abuja's wealth". news.bbc.co.uk. BBC News, Tuesday, 13 February 2007. 2007-02-13. Retrieved 2007-08-10.
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://hausa.legit.ng/news/1598418-ana-fama-da-tsadar-rayuwa-gwamnatin-legas-ta-kwace-motoci-kimanin-40-ta-bayyana-dalili/&ved=2ahUKEwjRsamO-fqGAxUdX0EAHY15CFwQxfQBKAB6BAgGEAI&usg=AOvVaw2HHG4B3BnU2aIP0dR1gKde
- ↑ Roman Adrian Cybriwsky, Capital Cities around the World: An Encyclopedia of Geography, History, and Culture, ABC-CLIO, USA, 2013, p. 2
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://guardian.ng/the-babangida-leadership-prescription/&ved=2ahUKEwjCtPDm-fqGAxXnT0EAHfSBDtwQxfQBKAB6BAgNEAI&usg=AOvVaw2PE_kvWnIeL0xUJSp-JQNj
- ↑ https://www.blueprint.ng/as-abuja-millennium-park-reopens/
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://hausa.leadership.ng/yajin-aiki-%25C6%2599ungiyar-%25C6%2599wadago-ta-rufe-filayen-jirgin-saman-legas-da-abuja/&ved=2ahUKEwibl-Ok-vqGAxXGTUEAHaoLAsQQxfQBKAB6BAgMEAI&usg=AOvVaw2s64GFONl9RO9mrE6eka7J
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.bbc.com/hausa/articles/cyrlpz03jp4o.amp&ved=2ahUKEwiyuP7K-vqGAxUiSEEAHZr4DpMQyM8BKAB6BAgLEAI&usg=AOvVaw1NLqlP-s1a7Q2bm8FpTfzu
- ↑ "Tarihin kafuwar Najeriya tun shekaru aru-aru" http://www.bbc.co.uk/hausa/news/2010/09/100914_early_history_nigeria50.shtml
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://hausa.legit.ng/news/1599342-mutane-sun-barke-da-murna-a-zamfara-bayan-dogo-gide-ya-dawo-yankinsu-sun-rera-masa-waka/&ved=2ahUKEwibtarx-vqGAxX0XUEAHSn_BcsQxfQBKAB6BAgFEAI&usg=AOvVaw0V8RJr3NIYs95kyUktuPqy
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://amp.dw.com/ha/fafutukar-samar-da-zama-lafiya-a-kaduna/a-54693251&ved=2ahUKEwjPyrGW-_qGAxXaWkEAHaAtAfsQyM8BKAB6BAgPEAI&usg=AOvVaw2nWaW9k2lTU_wPxPGHR5u7
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.vanguardngr.com/2024/06/tinubu-presides-over-fec-in-aso-rock/amp/&ved=2ahUKEwjqi_zI-_qGAxWERUEAHV3ODhYQyM8BKAB6BAgFEAI&usg=AOvVaw3MS-l8XZ8-gkTVWndjXxOj
- ↑ National Assembly | Federal Republic of Nigeria". www.nassnig.org. Retrieved 30 May2020.
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.thecable.ng/iswap-claims-responsibility-for-attack-on-military-checkpoint-near-zuma-rock/&ved=2ahUKEwjH1c7v-_qGAxVmQ0EAHSQZD_kQxfQBKAB6BAgJEAI&usg=AOvVaw3q5aZ-fZJk5bybIDdiub70
- ↑ Zuma Rock". Visit Nigeria Now. Retrieved 4 January 2022.
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.bbc.com/hausa/articles/ce9dg7z4qvyo.amp&ved=2ahUKEwiwr96V_PqGAxUhUUEAHVqTBy0QyM8BKAB6BAgGEAI&usg=AOvVaw0DG74-QvUbFX0WVt9-KApN
- ↑ Murray, Senan. "Life of poverty in Abuja's wealth." BBC. Tuesday 13 February 2007. Retrieved 12 September 2011.
- ↑ The Nigeria Capital City – AMLSN – Salt City 2020". Retrieved 23 January 2021.
- ↑ The Nigeria Capital City – AMLSN – Salt City 2020". Retrieved 12 May 2020.
- ↑ Aso Rock Declaration on Development and Democracy: Partnership for Peace and Prosperity | The Commonwealth". thecommonwealth.org. Retrieved 30 May 2020.
- ↑ The New Federal Capital". fcda.gov.ng. 2018. Archived from the original on 19 May 2020. Retrieved 5 January 2021.
- ↑ Abuja". www.oaugf.ng. Retrieved 5 January 2022.
- ↑ Abuja | Geography, Development, & Population | Britannica". www.britannica.com. Retrieved 5 January 2022.
- ↑ "Yusuf, Omotayo (1 October 2015). "#NigeriaAt55: Top 5 Reasons Nigeria's Capital Was Moved From Lagos To Abuja (PHOTOS.
- ↑ Moore, Jonathan (March 1984). "The Political History of Nigeria's New Capital". The Journal of Modern African Studies. 22 (1): 167–175. doi:10.1017/S0022278X00056846. JSTOR 160334. Retrieved 5 January 2022.
- ↑ Yusuf, Omotayo (1 October 2015). "Why The Capital Was Moved From Lagos To Abuja". Naija.ng – Nigeria news.
- ↑ Moore, Jonathan (March 1984). "The Political History of Nigeria's New Capital". The Journal of Modern African Studies. 22 (1): 167–175. doi:10.1017/S0022278X00056846. JSTOR 160334. Retrieved 5 January 2022.
- ↑ Moore, Jonathan (March 1984). "The Political History of Nigeria's New Capital". The Journal of Modern African Studies. 22 (1): 173. doi:10.1017/S0022278X00056846. JSTOR 160334. Retrieved 22 September 2020.
- ↑ Moore, Jonathan (March 1984). "The Political History of Nigeria's New Capital". The Journal of Modern African Studies. 22 (1): 173. doi:10.1017/S0022278X00056846. JSTOR 160334. Retrieved 22 September 2020.
- ↑ Moore, Jonathan (March 1984). "The Political History of Nigeria's New Capital". The Journal of Modern African Studies. 22 (1): 174. doi:10.1017/S0022278X00056846. JSTOR 160334. Retrieved 22 September 2020
- ↑ Elleh, Nnamdi (2001). Abuja, the single most ambitious urban design project of the 20th century. ISBN 9783897391659.
- ↑ Shuaibu, Umar. "Unsung heroes of Abuja master plan". Retrieved 22 September 2020.
- ↑ https://saharareporters.com/2023/08/31/uproar-abuja-minister-nyesom-wike-orders-task-force-destroy-500-impounded-commercial
- ↑ https://nigeriazipcodes.com/4049/local-government-area-in-fct/
- ↑ [[https://web.archive.org/web/20150214044550/http://www.abuja-ng.com/contactus.html Archived 2015-02-14 at the Wayback Machine
- ↑ https://www.villaafrika.com/fct-abuja-city-profile/