Abdullahi ɗan Muhammad
Abdullahi ɗan Muhammad | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Makkah, 610s |
Mutuwa | Makkah, 615 |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Muhammad |
Mahaifiya | Khadija Yar Khuwailid |
Ahali | Yaran Annabi, Rukayyah, Ummu Kulthum, Fatima, Zainab yar Muhammad da Ibrahim ɗan Muhammad |
Sana'a |
Abdullahi ɗan Muhammad (Larabci: عَبْد ٱللَّٰه ٱبْن مُحَمَّد) wanda aka fi sani da al-Ṭāhir (lit. 'the pure')[1] da al-Ṭayyib (lit. 'mai kyau')ya kasance daya daga cikin 'ya'yan Muhammad da Khadija. Ya rasu yana da kuruciya.[2] daya daga cikin yaran da Annabi Muhammad S.A.W ya haifa.
Tarihin Rayuwa
Cikakken sunansa Abd Allah bn Muhammad bn Abd Allah bn Shaiba. Mahaifinsa ya kasance ɗan kasuwa mai nasara kuma yana kasuwanci. Saboda kyawawan halayensa, Muhammadu ya samu laqabi da “al-Amin” (Larabci: الامين), ma’ana “aminci, amintacce” da “al-Sadiq” ma’ana “mai gaskiya” kuma an neme shi a matsayin mai sasantawa[3] . Sunansa ya jawo shawara a cikin 595 daga Khadija, ƴar kasuwa mai nasara. Muhammadu ya amince da auren, wanda bisa ga dukkan alamu ya kasance mai farin ciki. Qasim shine babban dan Muhammad da Khadija. Bayan Qasim an haifi yayansa mata hudu. An haifi Abd Allah a shekara ta 611. Shi ne auta a wajen Muhammad da Khadija.[4]
Annabi Muhammad (SAW.) ya ba shi sunan mahaifinsa. Abd Allah ya rasu a shekara ta 4 a shekara ta 615 miladiyya[2]
'Yan Uwan shi
'Yan uwan shi, su shida ne kamar haka;[5]
Qasim ibn Muhammad
Zainab bint Muhammad
Ruqayya bint Muhammad
Umm Kulthum bint Muhammad
Fatima bint Muhammad
Ibrahim ibn Muhammad
Manazarta
- ↑ "The Light of The Holy Qur'an (Sura Kauthar (The Abundance))". Archived from the original on 2007-09-27. Retrieved 2006-07-05.
- ↑ 2.0 2.1 Ahmed, Mahdi Rizqullah (2005). A Biography of the Prophet of Islam: In the Light of the Original Sources, an Analytical Study. Translated by Syed Iqbal Zaheer. Darussalam. p. 133. ISBN 9789960969022. Retrieved 17 September 2017.
- ↑ Khan, Majid Ali (1998). Muhammad the final messenger (1998 ed.). India: Islamic Book Service. p. 332. ISBN 978-81-85738-25-3.
- ↑ Esposito, John (1998). Islam: The Straight Path (3rd ed.). Oxford University Press. pp. 6, 9, 12. ISBN 978-0-19-511234-4.
- ↑ Ali, K. (2008). Smith, B.G. (ed.). Khadijah. Vol. 3. Oxford University Press. pp. 17–18. ISBN 9780 195148909